IQNA

Jami'an Tsaron Masar Sun kame Wasu Mabiya Tafarkin Iyalan Gidan manzo

12:48 - February 01, 2014
Lambar Labari: 1369023
Bangaren kasa da kasa, jami'an tsaron kasar Masar sun yi awon gaba da wasu mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah su goma sha shida a filin safka da tashin jiragen sama na birnin Alkahira bisa zargin cewa bas u da takardun shiga kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, a jiya jami'an tsaron kasar Masar sun yi awon gaba da wasu mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah su goma sha shida a filin safka da tashin jiragen sama na birnin Alkahira bisa zargin cewa bas u da takardun shiga kasar ta Masar.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan mataki ya zo ne sakamakon irin kura kuran da mahukuntan na Masar suke tafkawa wajen mayar da mutanen kasar makiyansu saboda dalilai na siyasa, duk kuwa da cewa kafin hambarar da gwamnatin da ta gabaci wannan, da cewa tana nuna bangaranci.

Yanzu haka dai mahuuntan kasar Masar suna ci gaba da farautar magoya bayan kungiyar yan uwa muuslmi da aka hambarar da gwamnatinsu wadda bat a wuce shekara guda da kafawa ba, kuma yanzu haka tsohon shugaban kasar yana tsare bisa zarginsa da tunzuru jama'arsa wajen kashe masu yi masa bore.

http://www.iqna.ir/fa/inter/News/1366996

Abubuwan Da Ya Shafa: Tafarkin
captcha