Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo On Islam cewa, da dama daga cikin malaman addinin muslunci daga kasashen nahiyar Afirka na ta kokarin ganin an kawo karshen kisan kiyashin da masu dauke da makamaio na mabiya addinin kirista suke yi wa mabiya addinin muslunci a kasar a cikin ‘yan lokutanan, lamarin da ya tayar da hankulan al’ummomin duniya.
A wani labarin kuma hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya World Food Programme ta bayyana cewar sakamakon habakar tashe-tashen hankula a sassa daban daban na kasar Afrika ta Tsakiya al’ummar musulmi ‘yan gudun hijira suna fuskantar matsalar karancin abinci, kamar yadda harkar shigar da kayayyakin abinci cikin kasar yana neman citura lamarin da ke kara haifar da matsalar karancin abinci a sassa daban daban na kasar.
Hukumar samar da abincin ta Majalisar Dinkin Duiniya ta kara da cewar a halin yanzu haka ‘yan dogayen motocin da suke ci gaba da safarar kayayyakin abinci daga kasar Kamarou zuwa birnin Bangui fadar mulkin kasar ta AFrika ta Tsakiya ba su samun damar shiga kasar sai da rakiyar dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika ta AMISCA.
Mayakan kiristoci sun tsananta kai hare-haren nasu kan musulmin kasar ne bayan da aka zabi shugabar kasa ta rikon kwarya wadda ta maye gurbin tsohon shugaban kasar na rikon kwarya, wanda shi ne musulmi na farko da ya taba rike kasar, wanda kuma kiristocin tamkar suna daukar fansa kan musulmi sakamakon hakan.
1376045