IQNA

Za A Gurfanar Da Wani Malamin Salafiyyah Saboda Kafirta Musulmi A Morocco

23:07 - February 18, 2014
Lambar Labari: 1376966
Bangaren kasa da kasa, mahukunta a kasar oroco na shirin gurfanar da wani malamin ‘yan salafiyya da ke kafirta musulmi a kasar saboda babban hadarin da yak e da shi ga zaman lafiya atsakanin al’ummar musulmi na kasar da suke rayuwa tsawon shekaru tare da juna duk kuwa da banbancin mazhabobi da ra’ayoyinsu.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga safin sadarwa na allafrica.fr cewa, a gobe ne mahukunta a kasar oroco na shirin gurfanar da wani malamin ‘yan salafiyya Abdulhamid Abu Na’im da ke kafirta musulmi a kasar saboda babban hadarin da yak e da shi ga zaman lafiya  atsakanin al’ummar musulmi na kasar ta Morocco da suke rayuwa tsawon shekaru tare da juna lami lafiya.
Malamn addinin muslunci a kasar suna yin kira ga dukkanin muslulmi da kirista da su kwana da sanin cewa ‘yan takafiriyya mutane ne da ba su dauke da wata akida ta wani addini, mutane da suke hankula daidai da irin ayyukansu na dabbanci kamar dai yadda babban sakataren kungiyar gwagwarmayar muslunci ta Lebanon ya fada.
Al’ummar kasar Morocco sun yi na’am da wannan mataki, kuma suna ci gaba da nuna goyon bayansu ga mahukuntan kasar kan su shiga kafar wando da kungiyoyin ‘yan salafiyya masu tsatsauran ra’ayi da suke kafirta musulmi, domin ta hakan ne kawai za a dakushe kaifin bala’in da suke dauke da shi kuma suke neman baza a shi a cikin al’ummar musulmi.
Kasar Morocco dai day ace daga cikin kasashen larabawa wadda akasarin mazauna cikinta musulmi mabiya tafarkin sunna, kuma suna zaune tare da mabiya wasu mazhabobin an daban ba tare da wata matsala ba, kamar yadda suke zaune tare da mabiya wasu addinan, kamar na kiristnaci ta kuma na yadudanci lami lafiya ba tare da wata matsala ba.

1376188

Abubuwan Da Ya Shafa: salafiyyah
captcha