IQNA

Ta'addancin 'Yan Ta'adda Ya Bata Sunan Addinin Musulunci A Idon Duniya

21:29 - February 20, 2014
Lambar Labari: 1377680
Bangaren kasa da kasa, Shugaban majalisar dokokin kasar Algeria ya bayyana ayyukan ta'addanci da wasu ke yi da sunan addinin musulunci da cewa hakan ya bata sunan addinin wannan addini mai tsarki a idon wadanda ba musulmi ba a wasu kasashen duniya.



Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a gaban taron shugabannin majalisun dokoki na kasashen musulmia  birnin Tehran Shugaban majalisar dokokin kasar Algeria Muhamamd Wuld Khalifa,ya bayyana ayyukan ta'addanci da wasu ke yi da sunan addinin musulunci da cewa hakan ya bata sunan addinin musulunci a idon duniya.
Daga cikin misalign day a bayar hard a yadda ta'addanci ya yi kamari a yankin kasashen arewacin Afirka, lamarin da ke neman ya gagari gwamnatocin wadannan kasashe a halin yanzu, inda masu dauke da makamai suke ta kara karfi tare da yin barazana ga tsaron al'ummoin yankin.
Sai dai duk da haka wasu masanan suna ganin daya daga cikin lamurran da suke taimakawa wajen yaduwar irin wadannan ayyuka na ta’addanci da rashin tsaro a wadannan kasashe har da bakar siyasa ta tattalin arziki da gwamnatocin wadannan kasashe suke aiwatarwa da ke cike da kura-kurai da kuma kara raunana irin karfi na tattalin arziki da suke da shi, lamarin da ke kara rashin aikin yi musamman a tsakanin matasa lamarin da ke sanya su shiga cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda da sauran ayyuka da suke barazana ga tsaro da zaman lafiyar wadannan kasashen.

1376803

Abubuwan Da Ya Shafa: algeria
captcha