Kamfanin dilalncin labaran qur'ani na Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga gidan talabijin na Aljazeera cewa, Rahotani daga tarayyar Nigeria na nuni da cewa a daren jiya litinin mayakan kungiyar Boko haram sun kai hari a wata Makarantar kwana a garin Boni yadi dake jahar Yobe a arewa maso gabacin kasar inda isar su ke da wuya suka sanya wuta a wannan makaranta sannan kuma suka kashe Daliban makarantar guda 43.
Majiyar asibitin Garin na Boniyadi ta tabbatar da wannan labari inda tace ya zuwa safiyar yau ta karbi gawawaki 43 na daliban wannan makaranta, a watan satumba na shekarar da ta gabata kungiyar ta boko haram ta kai irin wannan hari a makarantar kwana a jahar ta Yobe inda ta kashe kimanin Dalibai makarantar guda arba'in.
A wani labarin kuma Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta kirayi kasashen da ke makwaftaka da ita da su hada karfi da karfe wajen tunkarar kungiyoyin masu tsatsauran ra'ayin addini da ke dauke da makamai, da ke yin barazana ga tsaro da kuma zaman lafiyar yankin yammacin Afirka.
Ministan yada labarai na Najeriya Labaran Maku ne ya bayyana hakan a jiya a birnin Abuja fadar mulkin kasar, inda ya ce Najeriya na bukar yin aiki kafada da kafada da kasashe da ke makwaftaka da ita wadanda dukkaninsu renon kasar Faransa ne, musamamn ma kasar Kamaru daga cikinsu, wadda ke da iyaka da yankunan arewa maso gabacin Najeriya da ke fama da matsalar Boko haram.