Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Africanmanager cewa, an nada wakili na musamman na kungiyar kasashen musulmi a jamhuriyar Afirka ta tsakiya da nufin samun fahimtar juna da kuma dakushe yunkurin kawar da musulmi da ake yi a kasar wanda masu tsauran ra'ayn kiristoci suke yi.
Rahoton ya ce tsohon ministan harkokin wajen kasar Senegal Sheikh Tidjani Kagiyo ne aka nada, wanda kuma zai fara gudanar da ayyukansa nan bad a jimawa ba, kamar dai yadda majiyoyin kungiyar suka tabbatar da hakan.
Kasar Afirka ta tsakiya dai na fama da rikici na kabilanci da banbancin addini a cikin lokutan nan, wanda ya samo asali daga boren da aka yi a kasar ga wadanda suka yi juyin mulki wadanda kuma akasarinsu mabiya addinin muslunci ne, lamarin day a sanya kiristoci suke daukar fansa ta hanyar yin kisan gilla akan mabiya addinin muslunci dab a su jib a su gani ba.