Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Think Progress cewa, jami’a a kasar Amurka ta dakatar da shirinta na girmama wani dan kasar Somalia mai tsananin adawa da addinin muslunci wanda ya fito karara ya nuna cewaba shi babu addinin musulunci wanda yake kallonsa a matsayin addinin ta’addanci.
Bayanin ya ci gaba da cewa abin mutumin key i mai suna Aryan Hirsi Ali ya daga hankalin musulmi mazauna kasar Amurka matuka, wanda hakan ya sanya masana daga cikin yin rubutu da kuma aikewa da makaloli a kafafen yada labarai, domin nuna matsayinsu kana bin da yake yi, tare da tabbatar da cewa tuhumar da yake yi wa addinin muslunci ba gaskiya ba ne.
Yanzu haka dai wasu daga cikin musulmin kasar ta Amurka sun dauki matakin mayar da martini ta hanyoyi na yanar gizo wanda mutane suka fi dubawa, wanda kuma ko shakka babu hakan yay i tasiri wajen dakile yunkurin wanann jami’a wadda ta ke neman kara tunzura shi kana bin da yake yi.
1395237