IQNA

An Gudanar Da Tattaunawa Tsakanin Musulmi Da Kirista A Marakish

17:35 - May 04, 2014
Lambar Labari: 1403124
Sakamakon kisan kiyashi da ake yi wa musulmi A wasu kasashen Afirka an gudanar da zaman taro tsakanin mabiya addinin kirsta da kuma musulmi a birnin Marakish na kasar Moroco.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dilalncin Atlasinfo cewa Sakamakon kisan kiyashi da ake yi wa musulmi A wasu kasashen Afirka an gudanar da zaman taro tsakanin mabiya addinin kirsta da kuma musulmi a birnin Marakish na kasar Moroco da nufin tattauna wannan batu.

Duk da irin kiraye-kirayen da kungiyoyin kasa da kasa da ma gwamnatoci daban-daban suka yi wa mayakan kungiyar kiristoci na Anti Balaka a jamhuriyar Afirka ta tsakiya dangane da kisan gillar da suke yi wa musulmin kasar a kan su kawo karshen wannan mummunan aiki, amma mayakan kungiyar suna ci gaba da yin kunnen uwar shegu da wadannan kiraye-kiraye.

Inda koa jiya Lahadi fiye da musulmi 13000 ne aka tabbatar da cewa sun fice daga birnin Bangui sakamakon barazanar kisa da suke fuskanta daga ‘yan ta’adda na Anti Balaka, inda shedun gani da ido suka tabbatar da cewa wadannan musuli sun bar gidajensu da dukiyoyinsu, yayin da sojojin kungiyar tarayyar Afirka suka yi musu rakiya domin su fice daga birnin na Bangui, inda suka nufi arewacin kasar, da nufin isa kasar Chadi.

Bayanan sun tabbatar da cewa mayakan ‘yan ta’adda na Anti Balaka suna tsaye kusa da yankunan da musulmin suka bari, nan da nan kuma suka mamaye dukiyoyinsu da kaddarorinsu da ke wurin, da hakan ya hada har da gidajensu, ba tare da sojojin tarayyar Afirka ko na Faransa sun ce da su uffan ba.

A cikin makon da ya gabata ne dai jagoran mabiya addinin krista a kasar Afirka ta kudu Desmond Tutu yay i Allawadai da kisan muslmi da kiristoci ‘yan ta’adda na Anti Balaka suke yi wa musulmi a Afirka ta tsakiya, inda ya ce hakan ba koyarwar addinin kirista ba ce, tare da kiran gwamnatocin Afirka da su dauki kwararan matakai na kare rayukan musulmi a jamhuriyar Afirka ta tsakiya.

1402351

Abubuwan Da Ya Shafa: Marakish
captcha