Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na MASFON cewa, an gudanar da zaman fadar musulmi a Najeriya tare da halartar wasu daga cikin musulmin kasar, wanda hakan y aba su damar tatatuna batutuwa da suka shafi matsalolin da musulmin kasar suke fuskanta.
Babbar matsalar da ake fuskanta ta fuskar tsaro dai a Najeriya it ace matsalar kungiyar Boko Haram, kungiyar da take da alaka da masu tsatsauran ra’ayin wahabiyanci da kafirta musulmi.
A cikin lokutannan kungiyar ta kaddamar da hare-haren ta’addanci a cikin sassan kasar wanda hakan yay i sanadiyyar mutuwar mutane da dama akasarin wadanda kungiyar take kaiwa hare-hare kuwa musulmi ne mazauna yankunan arewacin kasar kasar.