Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, jagoran juyin juya halin musulunci Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana kur’ani a matsayin mai debe kewa ga ma’abotansa a lokacin da yake ganawa da makaranta da mahardata kur’ani mai tsarki da suka halarci gasar karatun kur’ani ta kasa da kasa da aka gudanar a birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, wanda aka kamala jiya.
A wani labarin kuma Jamhuriyar Musulunci ta Iran zata ci gaba da tsayawa da dukkanin karfinta wajen kalubalantar haramtacciyar kasar Isra’ila da take samun goyon bayan manyan kasashe masu girman kai a duniya.
A jawabinsa a taron juyayin cikan shekaru 25 da rasuwar Ayatullahi Imam Khomeini {r.a} da ya jagorancin kafa gwamnatin Musulunci a kasar Iran da aka gudanar a birnin Tehran a yau Laraba; Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullahi Sayyid Ali Khamene’i ya jaddada cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba zai yiyu ta taba sasantawa da azzalumai ba, kuma zata ci gaba da gwagwarmayar kare hakkin mutanen da ake zalunta a duniya.
Har ila yau Jagoran juyin juya halin na Musulunci ya fayyace cewar akwai yiyuwar cibiyoyin leken asirin kasashen makiya su ji cewa sun yi nasarar raunana fadakar Musulunci da ta kunno kai a wasu kasashen musulmi, amma hakan tunanin kuskure ne na makiya saboda akwai yiyuwar rusa wani bangaren fadakar Musulunci, amma tushensa yana nan tabbatacce kuma zai sake farfadowa a duk lokacin da ya dace.
1414065