IQNA

A Gobe Ne Za A Bude Babbar Gasar Kur’ani Ta Shekara A Kasar Malazia

23:59 - June 14, 2014
Lambar Labari: 1417546
Bangaren kasa da kasa, a gobe ne za a bude babbar gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasar Malazia da aka saba gudanarwa a kowace shekara tare da halartar makaranta daga kasashen duniya da dama.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo Bernama cewa, idan Allah ya kai mu gobe ne za a bude babbar gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasar Malazia da aka saba gudanarwa a kowace shekara tare da halartar makaranta daga kasashen duniya musamman ma kasashen musulmi daga cikinsu.
Wannan gasar dai it ace ta 56 da za a gudanar a kasar ta Malzia, tare da halartar makaranta da mahartdata su 77, daga kasashe 46, wadanda za su kara da juna, daga karshe kuma za a fitar da mutane 16 da za a baiwa matsayi na farko da na biyu da uku a dukkanin bangarorin da za a gudanar da gasar.
Bangarorin gudanar da gasar dai sun hada da karatun kur’ani mai tsarki a bangaren tartili da kuma tangimi, sai kuma bangaren hardar kur’ani, da hakan ya hada da bangaren hardar kurani baki daya, sai kuma bangaren masu hardar juzui, kama daga kasa zuwa sama, kamar dai yadda aka saba gudanar da wannan gasa a kowace shekara.
1417327

Abubuwan Da Ya Shafa: malazia
captcha