Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jagora cewa, A jawabin da ya yi a wajen wannan ganawar, Ayatullah khamenei ya taya al'ummar musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar jikan Manzon Allah, Imam Hasan al-Mujtaba (a.s). Har ila yau kuma yayin da yake magana kan irin muhimmanci amfanuwa da irin yanayi na kusaci da Ubangiji da ake samu a watan Ramalana musamman da dararen Lailatul Qadari, inda ya ce babban aikin mawaka shi ne: yin tasiri kwakwala da zukatan mutane da kuma samar musu da abubuwan da suke bukata na ciyar da ruhinsu gaba.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da kokarin Shaidanu na kutsawa cikin zukatan mutane da lalata musu irin munanan abubuwan, Jagoran juyin juya halin Musulunci cewa ya yi: mawaka suna da nauyi karfafa irin wannan ruhi da yanayi na kusaci da Allah da mutane suke da shi.
Har ila yau Jagoran yayi karin haske kan irin rawar da mawakan suke takawa wajen kyautata rayuwa da halayen mutane. Kamar yadda kuma yayi ishara da irin kokarin da makiya suke yi wajen lalata al'adu da dabi'un mutane inda ya ce mawakan suna da rawar da za su taka a wannan bangare.
Haka nan kuma yayin da yake magana kan irin mummunan yanayin da duniya take ciki da suka hada da irin hawar kawarar da masu tinkaho da karfi na duniya suke yi ga ‘yancin kai, dukiya, addini da kyawawan halayen al'ummomin duniya, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi ishara da halin da al'ummar Gaza suke ciki a halin yanzu na irin hare-haren da sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila suke kai wa can inda ya ce: A wasu lokuta saboda kashe wata dabba guda, wadannan mutane su kan tada jijiyoyin wuya da yada farfaganda, to amma irin hare-haren da ake kai wa Gaza da yayi sanadiyyar mutuwar sama da mutane 100 wanda mafiya yawansu yara ne da ba su ci ba su sha ba, ba ma wai kawai bai dame su ba, face ma dai Amurka da Ingila a hukumance suna goyon bayan hakan.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa; Hakikanin yanayin duniya a yau ita ce cewa ‘yan mulkin mallaka suna goyon bayan duk wani mummunan abu da fasadi da lalata matukar dai hakan zai taimakawa cimma manufofinsu. A daya bangaren kuma suna fada da duk wani abu mai tsarki da kima da ya ci karo da wadannan bakaken manufofin na su.
Daga karshe dai Jagoran ya bayyana jin dadinsa dangane da irin nasarori da ci gaban da mawakan suka samu.
Kafin jawabin Jagoran dai sai da wasu daga cikin mawakan suka gabatar da kasidoji da waken su.
1428823