Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ministan harkokin wajen Paqlastinu Riyad Maliki da sakataren kungiyar Larabawa Nabil Al-Arabi sun gana a birnin Alkahira, kungiyar ta Larabawan ta bayyana bakar siyasar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ke gudanarwa kan al'ummar Palasdinu musamman aiwatar da kisan kiyashi kan Palasdinawa, rusa musu gidaje da ci gaba da kame daruruwan mutane ciki har da jami'an Hukumar cin gashin kan Palasdinawa a matsayin manyan laifuka a fagen cin zarafin bil-Adama. Sakamakon haka kungiyar ta Larabawa ta bukaci kungiyoyin kasa da kasa gami da gwamnatocin kasashe da su hanzarta daukan matakin kalubalantar irin wannan ayyukan ta'addanci tare da bayyana haramtacciyar kasar ta Isra'ila a matsayin 'yar ta'adda da take tafka laifukan yaki kan al'ummar Palasdinu.
Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta fara kaddamar da sabbin hare-haren wuce gona da iri kan al'ummar Palasdinu ne tun bayan da'awar cewa; 'yan gwagwarmaya Palasdinawa sun sace wasu yahudawan sahayoniyya uku a kwanakin baya, sannan a bayan gano gawawwakin yahudawan ba tare da gudanar da wani bincike kan hakikanin abin da ya faru ba, gwamnatin haramtacciyar kasar ta Isra'ila ta dauki matakin tsananta kai hare-haren ta'addanci kan yankunan na Palasdinawa.
1429655