IQNA

Musulmin Ghana Sun Nuna Rashin Gamsuwarsu Da Taimakon Isra'ila

19:40 - July 17, 2014
Lambar Labari: 1430716
Bangaren kasa da kasa, a wani mataki na tozarci ga musulmin kasar Ghana jakadan haramtacciyar kasar Isra'ila a birnin Akra ya bayar da wasu 'yan buhunna na shinkafa da sukari ga limamin musulmi a birnin domin ya rabawa jama'a.

Kamfanin dillancin labaran kur'ani na Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ghana Web cewa, wannan lamari ya bakantawa musulmi da dama rai, baya ga cewa abin day a bayar baki bai wucu kilogram 200 ba, duka da shinkafar da sukarin domin a raba ma musulmin birnin Akra, a lokaci guda kuma ya yi hakan yana mai yin izgili da cewa suna taimakama musulmin Ghana da shinkafa da sukari a lokacin azumi a matsayin 'yan uwansu.

Da dama daga cikin musulmin Ghana sun bayyana cewa wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da Isra'ila take kashe fararen hula  a Gaza domin ta dauke hankalin musulmin Ghana daga irin ta'addancin da take aikatawa a kan fararen hula na yankin.

Yanzu haka dai adadin Palastinawa da suka yi shahada sakamakon hare-haren da jiragen yakin Haramtacciyar kasar Isra'ila suke kaddamarwa kan al'ummar ya kai dari biyu da ashirin da bakawai, yayin da wasu fiye da dubu daya da dari biyar suka samu raunuka.  
Kungiyoyin Palastinawa 'yan gwagwarmaya sun ci gaba  da antaya makaman roka a cikin biranen Isra'ila da sauran matsugunnan yahudawa 'yan kaka gida, domin mayar da martani kan kisan gilla da al'ummar yankin.
1429932

Abubuwan Da Ya Shafa: ghana
captcha