Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, majiyoyin asibiti a yankin Zirin Gaza sun ce akalla Palastinawa 7 ne suka yi shahada a daren jiya, sakamakon hare-haren da jiragen yakin Isra'ila suka kai a cikin garin Gaza da kuma yankin Khan Yunus, daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da kanan yara biyu da shekarunsu ba su wuce biyu zuwa shida ba, gami wata mata 'yar shekaru da haihuwa, wanda hakan ya cika adadin wadanda suka shahada 200 a cikin kwanaki 8 a yankin.
Kungiyoyin Palastinawa 'yan gwagwarmaya sun ci gaba da antaya makaman roka a cikin biranen Isra'ila da sauran matsugunnan yahudawa 'yan kaka gida, domin mayar da martani kan kisan gilla da al'ummar yankin.
A nata bangaren kungiyar Hamas a ta bakin kakakinta Sami Abu Zuhri, ta amince da wani kwaryakwaryan shiri na Majalisar Dinkin Duniya na dakatar da bude wuta a yau Alhamis har tsawon sa'oi biyar domin ayyukan jin kai.
1430312