IQNA

Iran Ta Yi Allah Wadai Da Hari Kan Zanga-Zangar Ranar Qudus A Nigeriya

20:36 - August 01, 2014
Lambar Labari: 1434789
Bangaren siyasa, Kasar Iran Ta Yi Allah Wadai Da Hari Kan Masu Zanga-Zangar Ranar Qudus A Garin Zariya Da Ke Nigeriya wanda hakan ya yi sanadiyyar shahadar mutane fiye da talatin.

Kamfanin dillancin abaran Iqna ya habarta cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da hare-haren wuce gona da iri da aka kai kan masu gudanar da zanga-zangar ranar Qudus a garin Zariya da ke tarayyar Nigeriya, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Malama Mardiye Afkham ta bayyana cewa; Kaddamar da harin wuce gona da iri kan masu zanga-zangar lumana ta ranar Qudus ta duniya ba abu ne da za a taba amincewa da shi ba, kuma mataki ne na cin zarafin bil-Adama.

Malama Afkham ta kara da cewa; Babban abin bakin ciki an kaddamar da harin wuce gona da irin ne kan al’ummar Nigeriya da suka fito domin nuna goyon bayansu ga al’ummar Palasdinu da ake zalunta tare da jaddada kin jinin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya, kuma harin da aka kai kan masu zanga-zangar a garin Zariya da ke jihar Kadunan Nigeriya baya da bambanci da irin wanda ake kai wa kan al’ummar Palasdinu.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ta jaddada cewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran tana bukatar ganin gwamnatin Nigeriya ta hanzarta daukan matakin zakulo wadanda suke da hannu a kai harin zalunci kan masu zanga-zangar ranar ta Qudus a garin Zariya tare da hukunta su.

1434446

Abubuwan Da Ya Shafa: iran
captcha