IQNA

An Bukaci A Yi Bincike Kan Kisan Da Isra'ila Ta Yi Wa Jami'an Kiwon Lafiya A Gaza

23:44 - August 09, 2014
Lambar Labari: 1437543
Bangaren kasa da kasa, kungigar Afuwa ta duniya ta bukaci da a gudanar da bincike dangane da hare-haren da sojojin Isra'ila suka kai kan ma'aikatan bayar da gaji a yankin Zirin Gaza.

A cikin wani bayanin da kungiyar ta afuwa ta kasa da kasa ta fitar a jiya, ta bayyana cewa akwai bukatar binciken gaggawa dangane da bayanai da ke cewa sojojin Isra'ila sun kai munanan hare a kan asibitoci da kuma motocin daukar marassa lafiya, tare da kashe likitoci da kuma masu gudanar da ayyukan agaji, kamar yadda wasu shedu masu karfi suka tabbatar da cewa sojin Isra'ila sukan hana kai dauki ga mutanen da ta kai wa hare-hare.
A jiya ne haramtacciyar kasar Isra'ila ta ci gaba da kaddamar da hare-harenta kan al'ummar gaza bayan karewa wa'adin tsagaita bude wuta na kwanaki uku, inda daga jiya zuwa ta kashe palastinawa 6, uku da cikinsu kananan yara.
Shugaban kasar Tunisia Munsif Marzuki ya fadi cewa, akwai wasu daga cikin shugabanni da sarakunan larabawa da suka nuna rashin amincewarsu da shirin dakatar da bude wuta a Gaza, yana mai yin ishara da cikakken goyon bayan da Isra'ila take samu daga wasu shugabanni da sarakunan larabawa a wannan yaki.
1436731

Abubuwan Da Ya Shafa: gaza
captcha