Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa nayanar gizo na Al-akhbar cewa, a jiya an gudanar da taron mahardata kur'ani mai tsarkia karon farko a kasar Mauritaniya tare da haatar mahardata daga sassa daban-daban na kasar, inda suka tatatuna muhimman batutuwa da suka shafi karatun kur'ani mai tsarki a kasar.
Taron dais hi ne irin na farko a kasar ta mauritaniya, kuma ya samu gagarumar karbuwa daga bangaroi da daman a masu gudanar da ayyuka da suka shafi kur'ani musamman makarantun harda, wadanda suka turo wakilansu a wurin, haka an kuma na ambata hanyoyi na zamani da za a rika yin amfani da su.
Daga karshen taron an fitar da wasu bayanai da suka kunshi wasu ka'idoji day a kamata a fara yin aiki das u domin samun ci gaba ta fuskar karatun kur'ani mai tsarkia fadin kasar, tare da jadda wajabcin yin aiki tukuru da kuma hakuri wajen jure wa ayyukan addini.
1437097