IQNA

20:37 - August 18, 2014
Lambar Labari: 1440693

Ana Samun Ci Gaba Ta Fuskar Muslunci A Kasar Swaziland Da Ke Afirka

Bangaren kasa da kasa, wasu bayanai sun tabbatar da cewa ana samun ci gaba a kasar Swazilnad da ke nahiyar Afirka a bangarori daban daban cikin sauri da hakan ya hada har da bangaren addinin muslunci sakamakon Karin wayewa da ake samu tsakanin al’ummomin nahiyar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga wasu kafofin yada labarai cewa ana samun ci gaba a Swaziland nahiyar Afirka a bangarori daban daban cikin sauri da hakan ya hada har da bangaren addinin muslunci.
A bangare guda kuma a jiya lahadi ne shuwagabannin kasashen kungiyar raya tattalin arzikin kasashen kudancin kafin haka dai ministocin harkokin wajen kasashe membobi a cikin kungiyar sun gudanar da tarurruka a ranakun ga watan Augusta da muke cikin don tattauna muhimman batutuwan da shuwagabannin zasu tattauna a kansu a garin Victoria Fall na kasar Zimbabwe.
Batutuwan wadanda suka hada da samar da aikin yi zuba jari da kuma shirin bunkasa tattalin arzikin kasashen yankin na tsawon shekaru biyar na daga cikin batutuwan da shuwagabannin zasu tattauna a kansu a cikin taron nasu na kwanaki biyu.
Banda wannan shuwagabannin kungiyar ta sadc suna wannan taron ne a dai lokacinda kungiyoyin kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa suka fitar da rahoton take hakkin bil’adamau a cikin kasashen yankin.
1439530

Abubuwan Da Ya Shafa: Swazilad
captcha