Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga jaridar Alraay cewa jami’ar musulunci ta Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar ta yi Allawadai da kakakusar murya dangane da harin da wasu ‘yan ta’adda da a ke sa ran ‘yan ISIS ne suka kai a cikin wani masallaci a birnin Dayali na mabiya sunna da nufin haddasa rikicin mazhaba a kasar.
Wani dan kunan bakin wake ya tarwatsa kansa a cikin Masallacin ‘yan Sunna da ke yankin arewa maso gabashin birnin Bagadaza na kasar Iraki lamarin ya janyo mutuwar masallata akalla sittin da hudu, majiyar tsaron kasar Iraki ta bayyana cewa; Wani dan kunan bakin wake da ya yi jigida da bama bamai ya tarwatsa kansa a tsakanin al’ummar musulmi da suke gudanar da sallar Juma’a a cikin Masallacin Mus’ab Bin Umair da ke kauyen Zurkush a lardin Diyala arewa maso gabashin birnin Baghadaza fadar mulkin kasar Iraki.
A bayan kai harin kunan bakin wake wasu mahara na daban sun bude wuta kan masallatan da suke cikin Masallacin lamarin ya janyo yawan mutanen da suka rasa rayukansu suka kai akalla 64 tare da jikkatan wasu adadi masu yawa.
Tun bayan da kungiyar ta’addanci ta daular Musulunci a Iraki da Sham wato Da’ish ta mamaye wasu yankunan arewacin kasar Iraki take aiwatar da kashe-kashen gilla kan al’ummar kasar musulminsu da kiristansu gami da sauran mabiya tsirarun addinai.
1442499