IQNA

Alamomin Muminai

IQNA - Tarin "Muryar Wahayi" gayyata ce zuwa tafiya ta ruhaniya da ban sha'awa tare da zaɓin mafi kyawun ayoyin Alqur'ani.

Idan Muka ɗanɗana wa mutãne wata rahama, sai su yi farin ciki da ita. To, idan wata masĩfa ta sãme su sabõda abin da suka kasance sunã aikatãwa, sai su yi baƙin ciki.

Shin, kuma ba su gani ba cẽwa lalle ne Allah Yanã azurta wanda Ya so daga yalwa, ko Ya tauye arziƙi? Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi ga mũminai. (Suratul Rum, aya ta 36-37).