Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na ISESCO cewa, kungiyar ta yi kakkausar suka da yin Allawadai da kisan wani dan jarida da haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi a yankin zirin Gaza tare da bayyana cewa hakan ya yi hannun riga da dukkanin dokoki na kasa da kasa.
A nasa bangaren tsohon shugaban kasar Afirka ta kudu ya jaddada kiransa ga al'ummomin kasar das u kaurace wa sayen kayayyakin da kamfanonin Isra'ila suke samarwa wadanda ake sayar da su a cikin kasar, tare da kiran jama a baki daya da su dauki matakai na goyon bayan al’ummar Palstinu.
Mbeki ya yi wannan kira ne a lokacin da yake gabatar da wata lacca da daliban jami'ar birnin Pretoria suka shirya a daren jiya domin nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu. Mbeki ya ce yana kira ga jam'iyyun siyasa da malaman addini da kuma kungiyoyin farar hula na kasar Afirka ta kudu, da su samar da wani shiri na kamfe a tsakanin al'ummar kasar na neman kaurace duk wasu kaya na Isra'ila, saboda kisan kiyashin da take yi wa fararen hula a Gaza.
A ranar Asabar da ta gabata ce kimanin mutane 50,000 suka gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a birnin Capetown domin yin Allawadai da Isra'ila da kuma kisan kiyashin da take yi kan mata da kananan yara a yankin Zirin Gaza.
1442458