Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, a zantawar da ta hada shi da mataimakin shugaban cibiyar da ke kula da harkokin kula da salla a Iran Sayyid Muhamamd Abdollahi ya bayyaan cewa, cibiyar tana gudanar da ayukanta yadda ya kamata a cikin nasara, domin ta samu nasarar horar da dubban mata da suke taimakon 'yanuwansu dangane da abubuwa da addini a fadin kasar.
A bangare guda kuma shugaban kasar Iran ya bayyana kisan kiyashin da yahudawa suke yi wa mata da kananan yara a gaza da cewa daidai yake da kisan dukkanin 'yan adam da ke bayan kasa.
Shugaban ya bayyana hakan ne yau a gaban daruruwan yara da iyayensu mata da suka yi jerin gwano a birnin tehran, domin nuna cikakken goyon bayansu ga al'ummar gaza musamamn 'yan uwansu mata da kananan yara da yahudawa ke yi wa kisan gilla, inda suke daga kwalaye da aka yi rubuce-rubuce da ke yin Allawadai da sahyuniyawa da kuma kasashen da ke mara mata baya a wanann aikin ta'addanci.
Tuni Iran ta aike da taimakon kayayyakin abinci da magunguna da sauran kayayyakin bukatar rayuwa ga al'ummar wadanda ake zalunta bayan killace su, amma mahukuntan Masar tare da hadin baki da sarakunan wasu kasashen larabawa, sun hana a shigar da kayan ta mashigar rafah da ta raba iyakokinsu.
1443116