IQNA

Gaza Ta Yi Nasara Ne Ta Hanyar Yin Gwagwarmaya Da Kuma Hakuri

23:44 - August 30, 2014
Lambar Labari: 1444728
Bangaren kasa da kasa, babban malamin addnin muslunci a kasar Bahrain Ayatollah Sheikh Isa Kasim ya ce al'ummar Gaza sun yi nasara a kan Isra'ila sakamakon gwagwarmayars da kuma hakurin da suka yi.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a hudubar Juma'a da ya gabatar a jiya malamin addnin muslunci a kasar Bahrain Ayatollah Sheikh Isa Kasim ya ce al'ummar Gaza sun yi nasara a kan Isra'ila sakamakon gwagwarmayars da kuma hakurin da suka yi a lokacin yakin da yahudawa suka kaddamar kansua  cikin kwanakin nan.

A jiya talata ce ma’aikatar harkokin wajen kasar Masar ta bada sanarwan cewa gwamnatin Benyamin Natanyahu ta Haramtaccoyar kasar Israila ta amince da sharuddan kungiyoyi masu gwagwarmaya da ita a yankin gaza na tsawon kwanaki 51 da suka gabata. A rahoton da tashar television na Skeynews ta nakalto daga ma’aikatar, tace ta amince da sharuddan Palasdinawan wadanda suka hada da bude tashar jiragen ruwa a yankin Gaza, Bude filin sauka da tashin jiragen sama, bude kofofin shiga yankin na Gaza da kuma kara fadada damar kamun kifi na Palasdinawa a yankin har zuwa kilomita 6 wanda kuma za’a kara tsawaita shi nan gaba. Ma’aikatar har’ila yau ta bayyana cewa za’a ci gaba da tattaunawar ba kai tsaye ba tsakanin bangarorin biyu bayan wata guda.

Da wannan yerjejeniyar dai muna iya cewa Palasdinawa a yankin gaza sun cimma bangare mai yawa da manufofnsu a wannan yakin wanda Israila ta takalesu da shi fiye da wata guda, mafi mihimmanci daga cikinsu shi ne kawo karshen killacewar da Isra'ila tayiwa yankin kimani shekaru 8 da suka gabata.

1444319

Abubuwan Da Ya Shafa: gaza
captcha