Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da wasu daga cikin manyan jami’an gwamnatin kasar, inda ya tabbatar da cewa makiya suna amfani da wadannan kungiyoyi na ‘yan ta’adda domin bata sunan addinin muslunci a duniya.
A lokacin da yake magana kan ummul aba'isin irin girgizar tushen tunani da aiki da ake samu a tsakanin al'umma da kuma irin babakeren da kasashen yammaci suka yi ga tsarin da ke gudanar da duniya a halin yanzu, Jagoran juyin juya halin Musuluncin cewa ya yi: A wannan lokaci mai muhimmanci, babban nauyin da ke wuya shi ne kara irin karfi da tsayin dakan da ake da su da suka ginu bisa tushen guda uku na asali, wato ‘ilimi da fasaha', ‘tattalin arziki' da kuma ‘al'adu'.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: hadin kai da aiki tare shi ne babbar bukatar da ake da ita a kasar Iran. A saboda haka nauyin da ke wuyan kowa shi ne goyon bayan gwamnati da bangaren masu gudanarwa.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya fara jawabin nasa ne da jinjinawa Ayatullah Mahdawi Kani, shugaban majalisar kwararrun wanda yake kwance a asibiti a halin yanzu inda ya yi masa addu'ar fatan samun sauki cikin gaggawa, kamar yadda kuma yayi addu'ar neman gafara ga ‘yan majalisar da suka rasu cikin watannin da suka gabata.
Yayin da ya koma kan lamurran da suke faruwa a duniya da kuma yankin gabas ta tsakiya kuwa, Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Abin da ke faruwa a halin yanzu lamari ne da ke nuni da sauyin da aka samu cikin tsarin da ke gudanar da duniya da aka kafa shi shekaru 70 din da suka gabata ta hannun kasashen yammaci da suka hada da Turai da Amurka; da kuma kafa wani sabon tsarin.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Sauyin da ake samu cikin shekarun baya-bayan nan a wannan yanki da kuma duniya, abu ne da a fili yake nuni da cewa tushen tsarin kasashen yammaci na cikin tsaka mai wuya da kuma girgiza.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Tsawon shekaru aru aru kenan kasashen yammaci suka dauka suna wasa da hankulan mutane ta hanyar amfani da take masu daukar hankali irin su ‘yancin kai, demokradiyya, kare hakkokin bil'adama da ba da kariya ga bil'adama, don tabbatar da tsarinsu a kan sauran bangarori na duniya da addinai daban-daban musamman addinin Musulunci. Abin bakin cikin kuwa shi ne cewa wasu a duniyar musulmi sun yaudaru da hakan, suna jin cewa al'adun yammaci yana da fifiko kan na su. har ya zuwa yanzu kuwa akwai masu wannan tunanin.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Idan da a ce al'ummomi, gwamnatoci ko kuma kungiyoyin ba su yaudaru da wannan ikirari na kasashen yammaci ba, sannan kuma suka tsaya kyam wajen tinkararsu, da ba su sami damar yin matsin lamba na siyasa da soji ba. A fili ana iya ganin wadannan matsin lamba a kan kasashe daban-daban ciki kuwa har da kasar Iran.
Ayatullah Khamenei ya kara da cewa: Kasashen yammaci suna ci gaba da tabbatar da wannan tsari na su cikin zukatan al'ummomi ta hanyar amfani da kafafen farfagandar da suke da su wadanda a kullum suna kara karfafa su da mayar da su na zamani. Suna ta kokari wajen ganin sun tabbatar wa da masana da ‘yan bokon wadannan kasashen cewa lalle tsarin kasashen yammaci ya dara sauran tsarurruka na duniya.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da irin girgiza da raunin da tushen tsarin kasashen yammaci ke fuskanta a halin yanzu, Jagoran yayi ishara da dalilai da kuma kalubalen da tsarin yammaci yake fuskanta a halin yanzu inda ya ce: Matsalar munanan dabi'u da ke ci gaba da yaduwa a kasashen yammaci bugu da kari kan rashin tsaro da damuwa ta ruhi musamman a tsakanin matasa, rugujewar tsarin iyali, daukar matsaya dake cike da kura-kurai dangane da lamarin da ya shafi mace bugu da kari kan yaduwar manyan munkarai irin su luwadi da madigo, dukkanin wadannan babbar barazana ce da ke tinkarar tsarin yammacin.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana irin ci gaba da samun riko da koyarwar addini musamman addinin Musulunci da kuma koyarwar Alkur'ani da ake samu a kasashen yammaci a matsayin kalubale na biyu da ke fuskantar tsarin yammacin don haka sai ya ce: kasashen yammacin da a kullum suke magana kan kiyaye ‘yanci da hakkokin bil'adama da demokradiyya, to amma a aikace suna ci gaba da take wadannan ikirari da suke yi, ta yadda a halin yanzu sun zamanto abin isgili a duk lokacin da suka yi magana kan wadannan abubuwan.
1447548