Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, a yau din dai Jagoran ya gana da wasu daga cikin jami’an Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kuma wasu gungun malamai na kasashen musulmi daban-daban da suka kai masa ziyara asibitin don isar da gaisuwarsu da kuma ganin halin da yake ciki.
Malaman da suka kai wa Jagoran ziyarar wani adadi ne na malaman kasashen musulmi daban-daban mahalarta taron kara wa juna sani na kasa na kasa da kasa mai taken “Malaman Musulunci Wajen Goyon Bayan Gwagwarmayar Palastinawa” wanda aka gudanar a nan Tehran inda suka bayyana farin cikinsu da yadda suka ga Jagoran yana ci gaba da samun sauki sannan kuma suka yi masa addu’ar samun sauki cikin gaggawa.
Malaman dai sun hada da mataimakin babban sakataren kungiyar gwagwarmatar lebanon wanda ya isar da sakon bababn sakataren kungiyar na gaisuwa da fatan samun sauki cikin gaggawa ga jagoran, hakan kuma malamai da dama daga kasashen duniya da suka halarci taron sun ziyarci jagoran tare da isar da sakonni na al'ummominsu gare shi.
1448822