IQNA

Furucin Jami’an Amurka Kan Yaki Da ISIS Yaudara Ce

13:06 - September 16, 2014
Lambar Labari: 1450723
Bangaren siyasa, jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khamenei ya fadi a lokacin da yake barin asibiti a ranar Litinin cewa abin da Amurka ke fadi na yaki da ‘yan ta’addan IS karya ce da yaudara.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin jagora cewa, a wata hira da yayi da dan jaridar gidan radiyo da talabijin na Iran kafin barinsa asibitin, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana farin ciki da jin dadinsa da yadda likitocin suka gudanar da aikin tiyatan yana mai cewa: A halin yanzu dai ina hanyar komawa ta gida bayan samun cikakkiyar lafiya, to sai dai kuma ina jin wani gagarumin nauyi a wuyana dangane da irin kauna da tausayawar da mutane suka nuna min tsawon lokacin da nake kwance a asibitin.
Yayin da yake bayyanar da godiyarsa maras iyaka ga al'umma, maraja'ai da manyan malamai, manyan jami'an gwamnati, ‘yan siyasa, masana da ‘yan wasa dangane da irin so da kaunar da suka nuna masa a lokacin da yake kwancen, Jagoran ya ce: Baya ga irin wannan kaunar da al'ummar Iran suka nuna, har ila yau al'ummomin sauran kasashen duniya ma sun nuna so da kaunarsu wanda hakan yana jaddada abin da na jima ina fadi ne na cewa al'ummar Iran suna da wani matsayi na musamman a tsakanin sauran al'ummomi.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Babu wani tsari ko wata kasa da take da irin wannan tasiri da alaka ta so da kauna, da akida da imani da sauran al'ummomin duniya a wajen kan iyakokinta (kamar yadda Iran take da shi).
Har ila ya Ayatullah Khamenei ya gode wa likitoci da malaman jiyyan da suka kula da shi tsawon zamansa a asibitin yana mai cewa: A lokacin da mutum ya ga irin wannan ilimi da kwarewa da likitoci da malaman jiyya na Iran suke da ita, lalle mutum ya kan yi farin ciki da kuma alfahari da irin wannan gagarumin arziki da ake da shi a bangaren kiwon lafiya wanda bangare ne mai muhimmancin gaske na rayuwar al'umma.
A wani bangare na hirar tasa, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi magana kan wani batun na daban inda ya ce: Tsawon wadannan ranakun da nake kwance a asibitin nan, na yi wani farin ciki wanda shi ne dangane da abubuwan da jami'an Amurka suke fadi dangane da fada da kungiyar Da'ish (ISIS), lalle hakan abin farin ciki ne.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana maganganun jami'an Amurka na fada da kungiyar Da'ish din a matsayin wani holoko da wasa da hankali kawai. Haka nan kuma yayin da yake ishara da kalaman sakataren harkokin wajen Amurka da kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka na cewa ba za su gayyaci Iran cikin fada da kungiyar Da'ish din da suka daura damarar yi ba, Jagoran cewa ya yi: Lalle abin alfahari ne a gare mu yadda Amurka ta yanke kauna kan shigowar Iran cikin wani aiki da ya saba wa doka sannan kuma na kuskure da suke son yi. Lalle babu wani abin da ya wuce hakan zama abin alfahari.
Daga nan kuma sai Ayatullah Khamenei ya yi karin haske kan abubuwan da suka faru kafin hakan don tabbatar da rashin gaskiyar wannan ikirari na Amurkawan na cewa ba za su gayyaci Iran wajen fada da kungiyar Da'ish din ba.
Jagoran ya ce: A daidai lokacin da Da'ish suka kaddamar da hare-harensu kan Iraki, jakadan Amurka a Iraki ya bukaci jakadanmu da ke Iraki da a shirya wata zamar tattaunawa tsakanin Iran da Amurka kan wannan kungiya ta Da'ish.
Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ci gaba da cewa: Jakadanmu a Iraki ya kawo wannan bukata (ta Amurkawan), wasu daga cikin jami'an gwamnati sun yi na'am da wannan tattaunawar, amma ni na ki amincewa, na ce ba za mu taba hada kai da Amurka cikin wannan lamarin ba. Don kuwa su masu bakar aniya ce kuma hannayensu dumu-dumu yake. Ta ya ya za a yi a irin wannan yanayin mu hada kai da Amurka.
Har ila yau kuma yayin da yake magana kan jawabin baya-bayan nan na sakataren wajen Amurka na cewa ba za su gayyaci Iran cikin hadin gwiwan da suke hadawa na fada da kungiyar Da'ish din ba Ayatullah Khamenei cewa ya yi: Shi kansa wannan sakataren wajen shi da kansa ya bukaci Dakta (Muhammad Jawad) Zarif (ministan harkokin wajen Iran) da cewa ku zo mu hada kai wajen fada da kungiyar Da'ish, amma Dakta Zarif ya ki amincewa da wannan bukatar.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Kai hatta ma mataimakiyar sakataren harkokin wajen Amurkan, wadda wata mace ce, kowa ya santa, a tattaunawar da ta yi da Malam Araqchi (mataimakin ministan harkokin wajen Iran), ta sake gabatar masa da wannan bukatar, amma Malam Araqchi ya yi watsi da wannan bukata tata.
Yayin da yake sake jaddada rashin amincewar Jamhuriyar Musulunci ta Iran dangane da hada kai da Amurka wajen fada da kungiyar Da'ish din, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce: A halin yanzu dai karya suke yi na cewa ba za mu gayyaci Iran cikin wannan hadin gwiwa na fada da Da'ish ba, alhali kuwa tun da fari Iran ta bayyanar da rashin amincewarta ta shigowa cikin wannan hadin gwiwa.
Ayatullah Khamenei ya jaddada cewar: A baya ma Amurkawan sun tada jijiyoyin wuya da hada wasu kasashe da nufin fada da kasar Siriya, amma babu wani abin da suka iya yi. Haka yanayin zai kasance dangane da kasar Iraki ma.
Ayatullah Khamenei ya ce Amurkawan dai ba da gaske suke yi ba dangane da batun fada da Da'ish da suke cewa suna yi inda ya ce: Su kansu Amurkawan da ma su ‘yan Da'ish din sun san cewa karya kashin bayan Da'ish din da aka yi a Iraki a baya, ba aiki ne na Amurka ba, face dai aiki ne na dakarun sa kai na al'umma da sojojin Iraki wadanda suka kaddamar da fada da kungiyar Da'ish din na hakika.
1450182

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha