Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Routledge cewa, shi littafi mai suna fitattun mata a cikin kur'ani da sunnah bisa mahangar mazhabar shia daya daga cikin daliban jami'ar Bermingham ne mai suna Rawand Osman ya rubuta shi a matsayin binciken da ya gudanar a karatunsa na digiri na uku da ya kammala a bangaren nazarin addinin muslunci a wannan jami'a.
Marubuci ya mayar da hankali matuka wajen daukar irin gagarumar gudunmawar da mata suka bayar a cikin addinin muslunci wajen ci gabansa a bangaren ilmi da tattalin arziki da kuma kayutata zamantakewar al'umma, har da yadda suka kasance a sahun gaba wajen kare addini a lokacin da bukatar hakan ta zama wajibi daga gare su, inda ya kawo bayanai dangan eda rayuwar manyan mata masu albarka da matsayi a cikin addinin muslunci.
Daga cikin matan da marubucin ya ambata tare da bayani kansu da kuma gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban addinin addinin muslunci, akwai Khadijah (S) matar manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka, sai kuma diyarsu Fatima Zahra (AS) da kuam diyarta Zainab (S) wadanda tarigin musulunci ba zai manta da su ba har kasa ta nade.
Haka nan kuma ya mayar da hankali ne a cikin binciken nasa a littafan shi'a domin su ne ska fi kawo bayani dalla-dalla kan su tare da fito da hakikanin gudunmawar ad suka bayar a dukkanin bangaro, lamarin day a sanya littafin nasa ya samu karbuwa matuka.