IQNA

Austria Na Da Nufin Fitar Da Tarjamar Kur’ani Domin Amfanin Musulmin kasar

3:02 - September 22, 2014
Lambar Labari: 1452354
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Austria na da nufin fitar da tarjamar kur’ani mai tsarki domin amfanin mabiya addinin muslunci da suke zaune a cikin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aslab News cewa, mahukuntan kasar Austria na da nufin fitar da tarjamar kur’ani mai tsarki domin amfanin mabiya addinin muslunci da suke zaune a cikin kasar da kuma kawar da gabar da wasu ke nuna ma musulmi da addinin muslunci.
Ministan harkokin wajen kasar ya ce masu nuna kyama ga addinin muslunci ko kuma tunzura wasu domin su kyamaci musulunci suna tafka babban kure, domin kuwa musulunci na hakika yana kira ne zuwa ga zaman lafiya, maimakon abin da wasu ke yin a ta’addanci da sunan musulmi, wanda acewarsa su kansu bas u fahimci addinin musulunci ba kuma bas hi ne suke wakilta ba, domin hatta sauran musulmi na duniya bas u amince da bin akidar ta’addanci da sunan addini ba.
Kasar ta fara karbar mabiya addinin muslunci ne tun a cikin shekara ta 1912, inda suka zauna  akasar a cikin ‘yancinsu kuma suke gudanar da harkokin addininsu ba tare da wata tsangwama daga mahukunta ko al’ummar kasar ba, in banda daga bayan da aka fara samun wasu masu kyamar musulmi wadanda su ma kadan matuka  akasar.
Ministan ya kara da cewa akwai musulmi kmanin dubu 500 a kasar, amma abin ban takaici wasu sun samu karkatattar fahimta kan musulunci inda suka rungumi ayyukan ta’addanci, inda yanzu kimanin musulmin kasar 140 suna Syria da Iraki suna kashe mutane da sunan jihadi a addinin muslunci.
1451941

Abubuwan Da Ya Shafa: austria
captcha