Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na kamfanin dilalncin labaran Saumariyya News cewa, manyan malaman addinin muslunci mabiya tafarkin sunna a Iraki sun yi kakkausar da yin Allah wadai da ayyukan kungiyar 'yan ta'adda ta daesh a kasar da ma sauran kasashen musulmi tare da tabbatar da cewa Amurka da Isra'ila ne suka kafa wannan kungiyar domin bata sunan addinin muslunci.
A nasa bangaren shugaban jamhuriyar muslunci ya ce 'yan ta'addan da suke cikin kasar Syria an san kasashen da suka fito, kuman san kasashen da suke ba su kudi da makami da kuma bude musu hanyoyin da suke shiga cikin Iraki da Syria, ya ce idan ba kawo karshen wannan ba harin Amurka da kawayenta a Syria ba zai kawo karshen 'yan ta'adda ba.
Shugaban ya kara da cewa tun kafin lokacin sun yi ta gaya wa kasashen yammacin turai da ma wasu kasashen yankin gabas ta tsakiya da suke ganin cewa za su yi amfani da 'yan ta'adda domin cimma manufarsu ta siyasa kan gwamnatin Syria da cewa wannan babban kure ne, domin kuwa wadannan 'yan ta'addan daga bisani ya juyo kansu, kuma shi ne abin da yake faruwa a halin yanzu.