Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam cewa, kungiyoyin musulmin kasar Kenya sun nuna rashin amincewarsu da batun wata doka da majalisar dokokin kasar ke bahasi kanta da ke neman haramta wa 'yan mata musulmi saka hijabin muslunci a makarantun boko a kasar.
Shugaban kungiyar musulmin kasar Kenya Abdulalh Godou ya bayyana cewa, za su dauki dukkanin matakan das ka dace domin dakile wannan yunkuri wanda ya sabawa dukaknin dokokin kasar na bayar da 'yancin gudanar da ayyukan addini ga dukaknin 'yan kasa ba tare da nuna wani bambanci ko takurawa ba, wanda kuma yin hakan takura ma musulmi ne bisa addininsu.
Ya kara da cewa bisa dokoki da kaidoji na addinin muslunci a duk lokacin da diya mace ta isa shekarun balaga, to daga lokacin ya zama wajibia kanta a cikin muslunci da ta rika rufe jikinta daga sauran mutane wadanda ba muharramanta ba, kuma tilasta yan mata musulmi das u daina saka hijabia makarantun tamkar cin zarafi ne a gare su.
Kasar Kenya dai tana da mutane da suka kai miliyan 36 miliyan 10 kuma mabiya addinin muslunci ne.