IQNA

Za A Gina Wata Cibiyra Hardar Kur’ani Mai Tsarki A Cikin masallacin Aqsa

23:30 - October 01, 2014
Lambar Labari: 1456413
Bangaren kasa da kasa, za a kafa wata cibiya ta hardar kur’ani mai tsarkia cikin masallacin Qods mai alfarma domin amfanin palastinawa da sauran musulmi mazauna birnin mai albarka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarat cewa, ya nakalto aga shafin sadarwa na ayanr gizo na Wafa cewa, ana shirin kafa wata cibiya ta hardar kur’ani mai tsarkia  cikin masallacin Qods mai alfarma domin amfanin palastinawa da sauran musulmi mazauna birnin wanda Isra’ila take kokarin haramta wa musulmi yancin gudanar da ayyukansu an ibada  acikinsa.
Bayanin ya ci gaba da cewa, an sanya hannun tsakanin jami’an gwamnatin kwqarkwaryan cin gishin kai ta Palastinawa da kuma jami’ai a  birnin Makka danagne da wannan batu, inda ake sa ran an ba da jimawa ba hukumar kula da ayyukan ilimi da al’adu ta kungiyar kasashen musulmi za ta dauki nauyin fara aiwatar da wannan shiri.
Birnin qods dai ya kasance mai dogon tarihi inda annabawan Allah suka gudnar da ayyukansu na isar da sakon ubangiji a cikinsa kamar dai yadda tarihin duniya ya tabbatar da hakan, haka nan kuma birnin da masallacin da ke cikinsa suna da matsayi a cikin addinin muslnci, inda masallacin ya zama alkibla ta farko ga musulmi.
1455703

Abubuwan Da Ya Shafa: aqsa
captcha