Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar pressTV cewa, yanzu haka ana shirin kafa wata runduna wadda za ta hada kasashen yankin tafkin Chadi domin yaki da kungiyar Boko Haram sun cimma hakan ne azaan da suka gudanar a birnin yamai na kasar Nijar.
A wani labarin kuma yan kungiyar Boko Haram sun kashe mutane bakwai a garin Ngamdu da ke jihar Borno a yankin arewa maso gabashin tarayyar Nigeriya ta hanyar datse musu kawuna.
Al’ummar garin Ngamdu da wata majiyar ta kusa da gwamnatin Borno da ta bukaci a sakaye sunanta sun bayyana cewa; ‘Yan kungiyar Boko Haram sun kai wani harin daukan fansa kan garin Ngamdu da ke jihar Borno a jiya Litinin, inda suka sace mutanen garin bakwai tare da kashe su ta hanyar aiwatar musu da yankar rago.
Wani dan garin na Ngamdu mai suna Musa Abor ya bayyana cewa; Wasu matanen garin ne suka tsinci gawawwakin mutanen bakwai a mace bayan ‘yan kungiyar Boko Haram sun aiwatar musu da kisar rashin tausayi ta hanyar raba kawunansu da gangan jikinsu.
Rahotonni sun bayyana cewar ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun kai farmaki kan garin na Ngamdu ne a matsayin harin daukar fansa sakamakon kashin da suka sha a garin makonni biyu da suka gabata da har ta kai ga halakar mayakansu 15, don haka suke zargin mutanen bakwai da hannu a kafa kungiyar banga domin farautar ‘yan kungiyar Boko Haram.
1458269