IQNA

Taron Idi Na Gadeer A Cibiyar Musulunci Ta Kasar Birtaniya

14:56 - October 11, 2014
Lambar Labari: 1459157
Bangaren kasa da kasa, a ranar Litinin mai zuwa za a gudanar da zaman taro na bukin idin Gadeer da harkokin muslunci a kasar Birtaniya tare da halartar malamai d akuma masana.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ic-el.com cewa, da yardarm Allah a Litinin mai zuwa za a gudanar da zaman taro na bukin idin Gadeer da harkokin muslunci a kasar Birtaniya tare da halartar malamai na addinin musulunci daga bangarori daban-daban, kuma za a fara ne da kimanin karfe 18:00 na yamma.

Shugaban cibiyar ya bayyana cewa za a gudanar da shirye-shirye na addini, da suka hada da bayanai da laccoci daga malamai da kuma masana, duk kuwa da cewa laccoci za su gudana ne a cikin harshen larabci, wanda za a tarjama ga wadanda bas u fahimtar harshen.

Daga cikin wadanda za su gabar da jawabai a wurin har da sheikh Rashad Al-ansari da kuma Sayyid Ja’afar Musavi, wadanda duk za su hallara domin jawabai da kuma kasidu na tunawa da zagayowar wannan rana mai tarin albarka da muhimmanci ga dukkanin al’ummar musulmi.

1458960

Abubuwan Da Ya Shafa: birtaniya
captcha