Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin Islamic Movment cewa za'a gabatar da shi ne na tsawon kwanaki uku a jere, a yau Asabar sannan gobe Lahadi sai kuma ranar Litinin a rufe, a lokacin zaman na yau wanda aka soma shi da misalin karfe hudu da rabi na yamma agogon Nigeria, mawakan harka ne suka fara kawata filin da gabatar da wake na yabon Imam Ali (AS)
Sai kuma bayan isowar Malam sai ya zauna ya soma gabatar da jawabi. A lokacin jawabin Malam ya fara ne da taya daukakin al'ummar musulmi murnar wannan gagarumin buki, sannan sai yaci gaba da bayani.
Wannan buki na idil Gadir yana gudana ne a Najeriya a daidai lokacin da ake gudanar das hi a wasu sassa na kasashen duniya.
1459130