Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO cewa, babban sakataren kungiyar Abdulaziz Bin Usaman Al-tuwaijari ya bayyana cewa wajibi ne a karfafa ayyuka na ilmnatarwa da bunkasa tunani da kuma mahanga irin ta musulmunci a tsakanin musulmi ta yadda hakan zai taimaka wajen daidaita tunaninsu bisa hakikanin koyarwar wannan addini.
Ya ci gaba da cewa wanann aiki ne da ya ratay kan malamai da kuma masana, domin kuwa da dama daga cikin musulmi ba su da masaniya kan wasu abubuwa da suka shafi addini ko matsayinsa kan lamurra da dama musamamn a wannan zamani da kuma yadda za su tafiyar da rayuwarsu ta zamantakewaa acikin kasashen duniya musamamn a kasashen dab a na musulmi ba, wannan ne ya sanya wasu ske daukar munan akidu da tsatsauran ra'ayi, wanda ke bakanta sunan addinin muslunci a duniya.
Al-tuwaijari ya ci gaba da cewa, a alokacin da musulmi suka samu cikkaen ilmi dangane da addininsu da kuma al'adunsu, to za su zama a bin koyi ga dukkanin al'ummomin duniya, domin addinin muslunci shi ne addinin da ke koyar da kyawawan dabiu da kuma kyakyawar mu'amamala, kuma dukkanin addinai za su ko yi das hi idan har musulmi suka siffantu da koyarwar a duk inda suke.