IQNA

Waki'ar Ghadir Ita Ce Ta Fito Da Hakikanin Musulunci Na Gaskiya

22:55 - October 14, 2014
Lambar Labari: 1460258
Bangaren siyasa, A ranar Litinin ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da dubban al’ummar Iran don tunawa da ranar Idin Ghadir mai girma inda ya bayyana ‘nada Amirul Muminin (a.s) a matsayin imami’ da kuma ‘muhimmancin da Musulunci ya ba wa lamarin siyasa da kuma gudanar da hukuma’ a matsayin ma’anoni guda biyu masu muhimmanci da suke cikin lamarin da Ghadir.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, yayin da yake sake jaddada muhimmancin da ke cikin hadin kai da aiki tare a tsakanin musulmi ya bayyana cewar: Duk wani mutum ko kuma duk wani aiki da zai sosa ran daya bangaren (musulmi) da kuma haifar da sabanin tsakanin Shi’a da Sunna, hakan taimako ne ga “Amurka, Ingila lalatacciya da kuma sahyoniyanci” wajen samar da jahilan kungiyoyi wadanda aka bar su a baya kana kuma masu kafirta al’umma.
Har ila yau a jawabin da ya gabatar a wajen wannan taron, Jagoran ya yi karin haske dangane da manufar ma’abota girman kan duniya wajen haifar da sabani tsakanin mabiya mazhabobin Musulunci musamman tsakanin Shi’a da Sunna inda ya ce: Ko shakka babu bayyanar sabani tsakanin musulmi wani lamari ne da zai sanya su lalata himma da kokarin da suke da shi cikin fada da rikici na cikin gida a tsakaninsu da kuma yin watsi da makiyansu na asali. Hakan kuwa ita ce damar manufar da ‘yan mulkin mallaka da ma’abota girman kan suke son cimmawa.
Ko shakka babu wani bangare na dalilan bayyanar irin wannan yanayi da duniyar musulmi take ciki yana komawa ne ga siyasar wasu gwamnatocin kasashen musulmin wadanda maimakon su ba da himma wajen tabbatar da hadin kai na kasa da na addini, sai suka zamanto masu aiwatar da siyasar manyan kasashen duniya. A hakikanin gaskiya sun zamanto masu aiwatar da siyasa da tsarin da wadancan mutane suke so ne a yankin gabas ta tsakiyan da sauran kasashen musulmi da kuma share fagen haifar da rarrabuwan kai ta addini da kabilanci. Daga cikin siyasar wadannan kasashen kuwa, ko shakka babu, akwai kirkiro kungiyoyin ‘yan ta’adda irin su Al-Qa’ida da Da’esh  don hana samuwar hadin kai tsakanin musulmi.
Ma’abota girman kan dai sun tsara wannan shiri na su ne ta yadda su da kansu musulmin ne za su lalata ko kuma alal akalla raunana irin dama da kuma karfin da suke da shi. Ta yadda a fili yake cewa ci gaban irin wannan yanayin zai tilasta wa duniyar musulmin, fada da junansu maimakon fada da makiyansu na asali wadanda su ne wadannan ma’abota girman kan da kuma yahudawan sahyoniya; kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Dubi da kyau da kuma idon basira cikin wannan lamari zai bayyanar da cewa Amurka da abokanta, suna ta kokari ne wajen haifar da kiyayya da gaba tsakanin musulmi da sunan fada da kungiyar Da’esh.
Jagoran ya bayyana cewa daya daga cikin dalilan da suka sanya ma’abota girman kai ba da himma wajen haifar da rarraba tsakanin musulmi shi ne fada da tunani mai jan hankali da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gabatar, inda ya ce: Bayan nasarar juyin juya halin Musulunci Amurka, sahyoniyawa da gwamnatin Ingila lalatacciya, wacce ta yi kaurin suna a fagen rarraba kan al’umma, sun ninninka irin kokarin da suke yi na haifar da rarrabuwa tsakanin musulmi da kawar da hankulan ‘yan Shi’a da Sunna daga makiyansu na asali. To sai dai kamar yadda Ayatullah Khamenein ya bayyana a halin yanzu wannan makirci na su na kirkiro kungiyoyin ta’addanci irin su Al-Qa’ida da ISIS ya fara komawa kansu, wato a takaice dai kaikayi ya fara komawa kan mashekiya.
A saboda hakan ne Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ce: Wajibi ne duk wanda yayi imani da Musulunci sannan kuma ya yarda da Alkur’ani mai girma, shin Shi’a ne shi ko kuma Sunna, wajibi ne ya farka ya kuma fahimci cewa abokiyar gabar Musulunci da musulmi ta hakika, ita ce siyasar Amurka da Sahyoniyawa.
Ko shakka babu wannan jawabi na Jagoran wani tushe ne cikin muhimmancin fahimtar makiya da kuma irin makirce-makircen da suke kullawa wanda a koda yaushe Jagoran ya sha bayanin hakan a matsayin wani lamari mai muhimmancin gaske cikin rayuwar musulmi inda a wannan karon ma Jagoran ya sake jaddada hakan a matsayin wani nauyi da ke wuyan dukkanin musulmi inda ya ce:  Wajibi ne Shi’a da Sunna su san cewa duk wani aiki ko kuma wata magana, ciki kuwa har da cin zarafin ababe masu tsarki na sauran mutane da ta yi sanadiyyar sosa rai da rura wutar fitina (a tsakanin musulmi), ko shakka babu hakan za ta amfani makiyan dukkanin musulmin ne.
1459737

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha