Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin jagora cewa, a lokacin da jagoran yake ganawa da palastinawa ya bayyana farin cikinsa mai yawa dangane da nasarar da ‘yan gwagwarmayar Gaza suka samu a kan haramtacciyar kasar Isra'ila a lokacin yakin kwanaki 51 da kuma irin gazawar da sahyoniyawan suka nuna wajen tinkarar al'ummar Gazan da aka killace su, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana wannan nasarar a matsayin daya daga cikin alamun da suke tabbatar da gaskiyar alkawarin Allah sannan kuma wata bishara ga gagarumar nasara mai zuwa, daga nan sai ya ce: Jamhuriyar Musulunci da al'ummar Iran suna alfahari da irin wannan tsayin daka na ku, sannan kuma muna fatan za ku ci gaba da samun irin wadannan nasarori har zuwa ga nasara ta karshe.
Ayatullah Khamenei ya bayyana yakin kwanaki 51 (da sahyoniyawa suke kaddamar kan al'ummar Gaza) da kuma irin tsayin dakan da al'ummar Gazan suka yi duk kuwa da karancin adadinsu da kuma ‘yan makaman da suke da su a gaban wata gwamnati maras tausayi da imani wacce take da duk wani nau'i na muggan makamai sannan kuma ga goyon bayan da take da shi, a matsayin wani lamari mai muhimmanci sannan kuma mai ban mamaki yana mai cewa: Bisa lissafi da sharhi na zahiri, haramtacciyar kasar Isra'ila tana iya gama wannan yakin cikin kwanakin farko-farko bisa la'akari da irin makamai da karfin da take da shi na zahiri. Amma daga karshe dai ta gaza wajen cimma manufofinta kana kuma ta mika wuya ga sharuddan dakarun gwagwarmaya.
Haka nan kuma yayin da yake ishara da alkawarin Allah na taimakon mujahidai, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Babu wata fassarar da za a iya ba wa irin hadin kan da mutane suka ba wa dakarun gwagwarmaya da kuma rashin gazawar da suka nuna duk kuwa da irin ruwan bama-baman da makiya suke yi musu da ya yi sanadiyyar mutuwar sama da mutane dubu biyu ciki kuwa har da wani adadi mai yawa na mata da kananan yara, in ban da tausayawa da kuma taimakon Ubangiji.
Ayatullah Khamenei ya ci gaba da cewa: Tabbatuwar wannan alkawari na Ubangiji a wannan fage (na Gaza) wata alama ce da ke nuni da cewa a nan gaba ma za a sami tabbatuwar wadannan alkawurra a fagage masu girma da fadi (sama da Gazan). Iko da kaddara ta Ubangiji ta sanya cewa a hannunku ne za a magance wannan matsala ta Palastinu.
A ci gaba da jawabin nasa, Jagoran yayi karin haske ne dangane da wajibcin yin taka tsantsan kan makirce-makircen makiya masu sarkakiya a kan kungiyoyin gwagwarmaya yana mai ishara da wasu batutuwa guda biyu masu muhimmanci.
Yayin da yake ishara da yiyuwar haramtacciyar kasar Isra'ila ta sake kawo wa Zirin Gaza hari, Ayatullah Khamenei ya bayyana cewar: Wajibi ne dakarun gwagwarmaya su kara karfi da irin shirin da suke da shi da kuma kara irin ajiyar (makaman) da suke da shi a Gazan.
Yayin da yake magana kan batu na biyun kuma, Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya bayyana wajibcin shigo da bangaren bakin kogi na yammacin Palastinu (yammacin kogin Jordan) cikin fadar da ake yi da sahyoniyawa ‘yan mamaya. Jagoran ya ci gaba da cewa: Yaki da haramtacciyar kasar Isra'ila, wani yaki ne mai ayyana makoma wanda da shi ne za a ayyana nauyi na karshe. A saboda haka wajibi ne a yi dukkanin abin da za a iya wajen sanya makiya cikin damuwa a yammacin bakin kogin kamar yadda suke cikin damuwa kan Gaza.
Daga karshe Ayatullah Khamenei ya bayyana yanayin da yankin Gabas ta tsakiya ke ciki da cewa wani yanayi mai sarkakiyar gaske yana mai cewa: Koda yake tabbas makomar abubuwan da ke faruwa a yankin nan wata makoma ce mai kyau kuma wacce take a fili. A saboda haka muna fatan Allah Madaukakin Sarki zai ba mu dacewa cikin dukkanin abubuwan da suke masu amfani ga al'ummar musulmi da al'ummar Palastinu da kuma kawo karshe makircin makiya.
Shi ma a nasa bangaren, babban sakataren kungiyar Jihadi Islamin Ramadhan Abdallah, ya bayyana farin cikinsa dangane da lafiyar da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya samu bayan tiyatar da aka yi masa inda ya ce: Dukkanin ‘yan'uwa ‘yan gwagwarmaya da kuma ‘yan kungiyar Jihadi Islami sun kasance suna maka addu'oin samun sauki a dukkanin lokutan sallolinsu. Muna fatan ganin ranar da mu da kai za mu yi salla a masallacin Al-Aqsa.
Haka nan yayin da yake karin bayani dangane da abubuwan da suka faru a yakin kwanaki 51 na Gazan, babban sakataren kungiyar Jihadi Islamin ya taya jagoran juyin juya halin Musuluncin murnar wannan nasarar yana mai cewa: Ko shakka babu an sami wannan nasarar ce albarkacin goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Saboda idan ba don taimako da shawarwarin Iran ba, da kuwa kungiyoyin gwagwarmaya ba su sami karfin da suke da shi da kuma yin nasara ba.
Ramadhan Abdallah ya ci gaba da cewa: Nasarar da kungiyoyin gwagwarmaya suka samu a Gaza, a hakikanin gaskiya nasara ce ga al'ummar Palastinu. Duk kuwa da irin hasara mai girma da aka yi a yayin wannan yakin, to amma irin hadin kai da hakuri da tsayin dakan da mutanen Gaza suka yi, wani abin kafa misali ne.
Ramadhan Abdallah ya bayyana maganar da Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi na wajibcin karfafa yankin Yammacin Kogin Jordan da makamai a matsayin wani lamari mai muhimmancin gaske wanda zai kara wa ‘yan gwagwarmayar irin karfin da suke da shi.
Yayin da kuma yake magana kan alkawurran da wasu kasashe suka yi na sake gina Zirin Gaza, babban sakataren kungiyar Jihadi Islamin ya ce: Mu dai ba mu damfara zukatanmu sosai ga wadannan alkawurra ba, face dai da Allah kawai muka dogara wajen cike gibin hasarar da haramtacciyar kasar Isra'ila ta haifar wa Gazan.