Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na ayanr gzio na CAIR cewa, an bude wani sabon shafin yanar gizo mai suna islamophobia.org a kasar Amurka wanda majalisar mabiya addinin muslunci a kasar ta dauki nauyin budewa domin yaki da akidar nan ta kyamar musulmi da addimin muslunci da wasu masu tsatsauran ra'ayi suke yi a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa babban dalilin bude wannan sabon shafi shi ne yadda wasu daga cikin masu adawa da musulunci a kasar suke ta kokarin yin amfani da hanoyoyi daban-daban musamman na sadarwa ta hanyar yanar gizo domin isar da bakaken manufofinsu ga al'ummar Amurka da ma sauran kasashen duniya.
Daya daga cikin muaten da suka bayar da gagarumar gudunmawa wajen an ganin an yada wannan shafi domin mutane su amfana da shia kasar ta Amurka ya bayyana cewa, akidar kymar musulmi a kasar ba wani sabon lamari ba ne, wadanda suke da wannan mummunar akida tun lokutan da suka gabata har yanzu ne ko kuma masu bin sahunsu, wanda kuma ba su masu rinjayea kasar Amurka ba, a kan hakan za su gaba da kokari domin ganin an wayar da kan jama'a dangane da addinin muslunci a kasar.