IQNA

Za A Gudanar da Wani Zama Dangane Da Binciken Ilmomin Kur'ani A Masar

23:16 - October 26, 2014
Lambar Labari: 1464219
Bangaren kasa da kaa, za a gudanar da wani zama a kasar Masar wanda zai dubi danagne da hanyoyin bicike na ilmomi da ke cikin alkur'ani mai tsarki.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sada Balad cewa, a cikin wannan mako ne za a gudanar da wani zama a kasar Masar wanda zai dubi danagne da hanyoyin bicike na ilmomi da ke cikin alkur'ani mai tsarki kasantuwarsa littafin day a kunshi dukkanin bangarori na ilmi wadanda dan ya rika da kuma wadanda bai riska ba, da kuma wadanda a halin yanzu ta hanyar bicike ne ake gano su.

Bayanin ya ci gaba da manufar wannan shiri ita ce kara fitar da abubuwa da daman a ilmi dag cikin alkur'ani mai tsarki wadanda ba a kai ga fitar das u, ko kuwa wadanda ya yi bayani kansu amma ba azauna an gudanar da bincike a kansu, wanda kuma masana za su iya taka gagarumar rawa ta wannan fuska.

Wannan taro dai zai samu halartar masana da kuma masu bicike dag a kasashen duniya daban-daban da suka hada da kasashen musomi da kuma na larabawa gami da wasu daga cikin kasashen yammacinturai, wadada suke da shawar shiga cikin irin wadannan ayyuka na binciken ilimi da ke cikin littafin alkur'ani mai tsarki.

Kasar Masar dai na daga cikin kasashen da suke maya da muhimmanci ga wannan bangare, musamman ma ganin yadda ake samun karuruwar masu shiga cikin harkokin kur'ani a kasar fiye da kowane lokaci.

1463577

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha