IQNA

An Kammala Wata Gasar Kur’ani Mai Tsarki A Kasar Mauritaniya

23:00 - October 27, 2014
Lambar Labari: 1464663
Bangaren kasa da kasa, an kamala wata gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki da aka shirya a kasar Mauritaniya a birnin Nuwakshout fadar mulkin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Misral yaum cewa a yau ne aka kamala  gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki da aka shirya a birnin Nuwakshout na kasar Mauritaniya.
A bangare guda kuma an gudanar da taron girmama wadanda suka kwazo a gasar karatun kur'ani mai tsarki wadda aka gudanar kai tsaye ta gidajen talabijin na kasar Mauritanita da ake kira gasar kur'ani ta talabijin a kasar, wadda aka saba yi a cikin 'yan shekaru baya-bayan nan.
Shugaban hukumar kula da ayyukan kur'ani a ma'akatar kula da harkokin addinin muslunci a kasar Sidi Muhammad wold Sheikh shi ne ya jagoranci gudanar da wannan gasa, wadda ta kasance a sahun gaba a cikin ayyukan da ake gudanarwa a halin yanzu a bangaren da ya shafi kur'ani mai tsarki a kasar.
Wasu daga cikin bangarorin da suka gudanar da wannan gasa kuwa har da dattijai wadanda suka kasance a sahun gaba  acikin mahardata na kasar, wadanda kuma sun samu kyutuka na girmama sakamakon kwazon da suka nuna a wanann gasa, da kuma irin hidimar da suka yi kur'ani ami tsarki na tsawon lokaci a rayuwarsu.
1463892

Abubuwan Da Ya Shafa: mauritania
captcha