Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, jagoran ya bayyana hakan ne yau a lokacin da yake ganawa da jam'ai a bangaren aikin hajji na kasar, inda ya tabbatar musu da cewa aikin hajji a matsayinsa na daya daga cikin manyan ayyukan ibada kuma rukuni daga cikin manyan rukunai na musulunci, babbar hanya ce ta hada kan al'ummar musulmi, ta yadda za su zama tsintsiya daya madaurinki daya.
Ayatollah Sayyid Khamenei ya kara da cewa abin da ake nufi da hadin kai tsakanin dukkanin muslulmi ba shi ne wani ya bar abin da yake yi a zo hadu a kana bin da wani yake yi ba, abin nufi shi ne musulmi su hadu a kana bin da yahada na muslunci, wanda dukkaninsu suka yi imani das hi, kuma su yi aiki a kansa, abin day a shafi fahimta kan wasu lamurra kuma, kowa sai ya yi aiki da iliminsa da abin da ya fahimta a kefe, amma a matsayi na al'umma a hadu a kan abu guda wanda kowa ya yi imani da shi, ya ce da musulmi za su yi haka da sun zama al'umma mafi karfi a duniya.
A ci gaban bayanin nasa, jagoran ya jaddada wajabcin yin aiki tukuru domin fadakar da al'ummomin duniya irin babban makircin da ake shiryawa al'ummar musulmi ta hanyar haifar da fitintu a tsakaninsu da nufin raba kansu, domin su yi rauni ta yadda makiya za su ci karensu babu babba, kamar yadda kowa yake shedawa a halin yanzu a wanann duniya.