Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar talabijin ta Almanar cewa, jam’iyyar tauhid ta kasar Lebanon ta yi kakakusar suka da yin Allawadai dangane da rufe masallacin Quds da yahudawan sahyuniya suka yi a cikin wannan mako domin hana musulmi gudanar da salla a cikinsa.
Rahotanni sun ce an sake bude masallacin bayan rufe shi da ‘yan sahayoniya su ka yi a jiya alhamis. Sanarwar rufe masalacin na kudus da ‘yan sahayoniya su ka yi a jiya alhamis ya fusata mazauna birnin na Qudus,kamar kuma yadda gwamnatin Palastinawa ta bayyana shi a matsayin shelanta yaqi akan al’ummar Palastinu da kuma musulmi.
Kamfanin Dillancin Labarun ya nakalto cewa; An sami dawowar kwanciyar hankali a cikin birnin na Qudus bayan da a wunin jiya aka yi batakashi tsakanin matasa da jami’an tsaron haramtacciyar kasar Isra’ila. Sai dai duk da bude masallacin kudus, yan sahayoniya sun gindaya sharadin cewa wadanda shekarunsu ba su kai 50 ba ba za su shiga masallacin ba domin yin salla.
Keta hurumin masalalicn Kudus dai ya zama wani abu da yahudawa ‘yan share wuri zauna su ke yi a kowace rana ta Allah ta hanyar kutsawa cikinsa. Wannan dai shi ne karo na biyu da aka rufe masallacin na Kudus, tun wanda ya faru a shekarar dubu da dari tara da sabain da shida.
1466155