Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na INA cewa, a kasar Moroco za a gudanar da wani taro a kasar Moroco wanda zai yi dubi kan irin shishigin da haramtacciyar kasar Isra’ila take yi kan masallacin Qods mai alfarma kamar dai yadda majiyoyin suka tabbatar.
A bangare guda kuma babbar jami’ar dflomasiyar turai ta yi kira da a samar da kasar Falasdinu domin kawo karshan rikici a yankin gabas ta tsakiya, wannan kwa a daidai lokacin da ake ci gaba da samun barkewa rikici a birnin Kudus.
Ta fadi haka ne a ziyarar da ta kai a zirin Gaza inda tace bai kamata ba a zuba ido wa wadanan kasashe da ke fama da rikici ba, don haka zata tuntunbi duk kasasshen kungiyar tarrayya Turai domin kawo karshen wanan rikici.
Sai dai a nasa banagaren Shugaban Falasdinawa yace su na kan shirin tura dabtarin kudiri zuwa Majalisar Dinki Duniya, domin kawo karshan iko da Isara’ila ke yi da yankunansu da kuma wasu kadarorin su.
Ya zuwa yanzu dai kasar Suedin ce kasa turai ta farko data amunce da kasar Falastinu bayan kasashe 134 da suka amunce da hakan a duniya.
1470989