IQNA

Mohammad Sarafraz Sabon Shugaban Hukumar Radiyo Da Talabijin Na Kasar Iran

22:29 - November 09, 2014
Lambar Labari: 1471532
Bangaren siyasa, A cikin wata sanarwa da ya fitar a yau din nan Asabar (08-11-2014) Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya nada Dakta Muhammad Sarafraz a matsayin shugaban hukumar gidan radiyo da talabijin ta Iran.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jagora cewa yayin da yake ishara da irin gagarumin nauyin da ke wuyan hukumar radiyo da talabijin din wajen kiyayewa da kuma fadada ‘yanci da matsayi da al’adu da matsayin juyin juya halin Musulunci na Iran ya ke da shi, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Hukumar gidan radiyo da talabijin, saboda irin nauyi na ‘shiryarwa da kuma tsara al’adu da tunanin al’umma da take dauke da shi’ tana da gagarumin aiki a wuyanta na yada addini, kyawawan halaye, fata, wayar da kai da yada salon rayuwa na Musulunci da Iran a tsakanin al’umma. Haka nan kuma a matsayinta na na’ura mai juya da kuma karfafa ci gaban kasa, tana da nauyin wayar da kan al’umma, haka nan kuma da taimakon jami’ai masu gudanar da kasa wajen tabbatar da manufofi da aiwatar da siyasa ta gaba daya ta wannan tsari da kuma tsarin ci gaban kasa na gaba daya.
Abin da ke biye fassarar sanarwar nadin ne da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya fitar:
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai
Mai girma, Malam Muhammad Sarafraz (Allah ya kara masa dacewa)
Sakamakon cikan wa’adin karshe na shugabancin mai girma Injiniya Sayyid Izzatullah Zarghami, wanda ke cike da kokari da aiki tukuru, sannan kuma bisa la’akari da irin dacewa, fahimta da kuma irin doguwar kwarewar da kake da ita a fagen shugabanci a hukumar gidan radiyo da talabijin ta kasa da kuma masaniyar da kake da ita dangane da ayyukan wannan hukuma mai matukar muhimmanci, don haka na nada ka a matsayin shugaban hukumar gidan radiyo da talabijin ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran na wa’adin mulki na shekaru biyar.
Hukumar gidan radiyo da talabijin dai, bisa la’akari da nauyi mai girma da muhimmancin gaske da ke wuyanta na “shiryarwa da kuma tsara al’adu da tunanin mutane” tana a matsayin wata makaranta ce. Haka nan kuma bisa la’akari da ayyuka da tsare-tsarenta na isar da sako, tana da nauyi na fadada addini da kyawawan halaye da fata da fahimta da kwadaitar da salon rayuwa irin ta Musulunci da al’adu na Iran a tsakanin al’umma a wuyanta. Babban nauyin da ke wuyan hukumar gidan radiyo da talabijin ta kasa a wannan lokacin, shi ne kiyayewa da karfafa ‘yanci na al’adu da matsayi na juyin juya halin Musulunci na Iran. Azama ta kasa da farin ciki da nishadi na juyi tsakanin dukkanin al’umma a fagen isa ga manyan manufofin tsarin Musulunci karkashin fahimta da gagarumar masaniya da mutane suke da ita tana bukatar haduwa da mabubbuga ta tunani na hakika na addini da masoya wannan juyi na Musulunci. Har ila yau kuma hukumar gidan radiyo da talabijin a matsayinta na wata cibiya mai motsawa da kwadaitar da ci gaban kasa, tana da nauyi na goyon baya da ba da taimako irin na kafafen watsa labarai a fagen janyo hankulan mutane da kuma taimakon masu gudanar da kasa wajen tabbatar da manufofi da kuma gudanar da manyan siyasosin wannan tsari da tabbatar da siyasar ci gaban kasa da aka tsara. Ga tsare tsare da hanyoyin da ya kamata a bi wadanda, insha Allah, za su taimaka wa hukumar gidan radiyo da talabijin din sauke wannan nauyi da ke wuyanta.
Daga karshe wajibi ne in jinjina da kuma gode wa mai girma Injiniya Zarghami da abokan aikinsa wadanda suka sami damar ciyar da hukumar gidan radiyo da talabiji ta kasa din gaba da kuma taka gagarumar rawa a fagage daban-daban na siyasa, zamantakewa da al’adu.
Ina rokon Allah Madaukakin Sarki da ya taimaka maka a wannan aikin mai girma da tsananin muhimmanci bisa la’akari da irin matsayinka na daya daga cikin iyalan shahidai masu girma da daukaka na juyin juya halin Musulunci. Haka nan kuma zan ci gaba da yi muku addu’a kai da abokan aikinta.
Sayyid Ali Khamenei
15, Aban, 1393 (Hijira Shamsiyya)
(6, Nuwamban, 2014)

1470961

Abubuwan Da Ya Shafa: Rahbar
captcha