Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Kullul Iraq cewa, Ayatollah Sayyid Ali Sisatani babban malamin addinin muslunci na kasar Iraki ya mika sakon ta’aziyarsa ga al’umma da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukansu a taron ranar Ashura a yankin Ihsa na gabacin kasar Saudiyya bayan da wasu yan ta’adda suka kai hari a kansu.
Ayatollah Sistani ya bukaci mahukunta akasar ta Saudiyya da su dauki dukkanin matakan da suka dace domin gano wadanda suke da hannu wajen kai harin ta’addanci a kan masu taron Ashura domin tabbatar da cewa an yi musu hukuncin da ya dace musamman ma ganin sun yi kisan kai.
Kwana biyu bayan harin jami’an tsaron Sudiyya sun sanar da kamo mutanen da su ka kai harin ta’addanci akan ‘yan shiyar da ke juyayin Ashura a wani kauye da ke gabacin kasar, an kame mutane tara wadanda su ka kai harin a yankin Ihsaa da ke gabacin Saudiyya a daren jiya wanda ya yi sanadin shahadar mutane 7 da jikkata wasu, mafi yawancinsu kananan yara.
Majiyar ta ce; mutanen sun shirya kai wasu hare-haren a cikin garuruwan Khubar da Qatif da ke gabacin kasar inda mafi yawancin mutanensa ‘yan shi’a ne. Harin na jiya ya zo ne dai a lokacin da ake rayuwa cikin zullumi a gabacin Saudiyya din, bayan yanke hukumcin kasa da wata kotun kasar ta yi wa daya daga cikin fitattun malaman mazhabar iyalan gidan manzo.
1471388