IQNA

Kowa Ya Sani Cewa Daesh Ba Musulmi Ba Ne Kuma Ba Musulunci Suke Yi Ba

2:48 - November 10, 2014
Lambar Labari: 1471551
Bangaren kasa da kasa, ya zama wajibi kowa ya sani cewa yan ta’addan daesh da ake kira yan ISIS ba musulmi ba ne kuma a bin da suke yi a Iraq da Syria ba shi da wata alaka da addinin mulunci ko alama.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarat cewa, wani fitaccen dabn siyasa mai rajin kare hakkin yan adam a kasar Birtyaniya ya ce kowa ya sani cewa yan ta’addan daesh ba musulmi ba ne kuma a bin da suke yi  ba shi da wata alaka da addinin mulunci da kuma musulmi.
Sojojin kundumbala na kasar sun sanar da kwace kauyuka sha shida a yau Lahadi daga hannun mayakan 'yan ta'adda na ISIS a arewacin kasar, tare da kashe adadi mai yawa na 'yan ta'addan tare da kame wasu.
Mai aiko wa tashar talabijin ta alam rahotanni daga yankunan arewacin kasar iraki ya bayar da rahoton cewa, tun kimanin makonni biyu da suka gabata ne sojojin na kasar Iraki tare da wasu dubban sojin sa kai na matasan 'yan sunna da shia da kuma Kurdawa suke ci gaba da kaddamar da farmaki kan mayakan 'yan ta'adda na ISIS a yankunan da suka kwace iko da su a arewacin kasar, inda suke samun gagarumar nasara a kan 'yan ta'addan.
Rahoton ya ce a nasu bangaren 'yan ta'addan suna ci gaba da bin sawun wasu kabilun 'yan sunna a wasu yankunan arewacin kasar suna yi musu kisan gilla, saboda sun ki ba su hadin domin cimma manufarsu ta kafa abin da suke kira daular musulunci.
Shi ma a ganawarsa da babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi a gefen zaman taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya; Shugaban jamhuriyar musulunci ya yi nuni kan mummunar illar da bullar akidar tsaurin ra’ayin addini da zubar da jinin bil adama da sunan Musulunci suka yi a tsakanin al’ummar musulmi musamman a kasar Siriya da hakan ya zame wani babban barazana ga hakikanin koyarwar addinin Musulunci.
1471424

Abubuwan Da Ya Shafa: daesh
captcha