Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ofishin jagora cewa, a safiyar yau Litinin ce Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gana da mataimakin shugaban kasar Iraki Dakta Nuri al-Maliki da ‘yan tawagarsa da suka kai masa ziyarar ban girma. A yayin wannan ganawar, Jagoran ya jinjinawa irin jaruntaka da tsayin dakan da Nuri al-Malikin ya nuna a yayin da yake rike da matsayin firayi ministan kasar Irakin da kuma gagarumar hidimar da ya yi wajen tabbatar da tsaro da ‘yanci da kuma ci gaban kasar Iraki inda ya ce masa: Yayin mika mulkin da ya gudana a kasar Iraki, lalle ka aikata gagarumin aiki wajen hana faruwar rikici da rashin tsaro a kasar Iraki. Ko shakka babu ba za a taba mancewa da wannan babban aikin a kasar Iraki ba.
Yayin da yake ishara da irin masaniyar da Dakta Nuri al-Malikin yake da ita kan yanayin kasar Irakin da kuma matsalolin da take fuskanta, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewar: Kokarin da kake yi wajen taimakon sabuwar gwamnatin Dakta Haidar al-Ibadi da kuma kokari wajen samar da hadin kai tsakanin al’ummar Iraki, lalle hakan wani lamari ne mai kyaun gaske, da wajibi ne ka ci gaba da yinsa.
Shi ma a nasa bangaren, mataimakin shugaban kasar Irakin Nuri al-Maliki, ya bayyana gagarumin farin cikinsa da ganawa da Jagoran juyin juya halin Musulunci yana mai cewa: A koda yaushe Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kasance mai taimakon gwamnati da al’ummar Iraki a fadar da take yi da ayyukan ta’addanci da kuma tsoma bakin ‘yan kasashen waje.