IQNA

Ya Kamata Koyar Da Addinin Musulunci Ya Zama Na Hadin kai Ba Rarraba Ba

16:31 - November 13, 2014
Lambar Labari: 1472860
Bangaren kasa da kasa, tsohon firayi ministan kasar Malaysia ya yi kira dangane da muhimamncin yin amfani da hanyar koyar da addinin muslunci ta zama ta hadin kai tsakanin al’umma ba rarraba kanta ba.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar New Strait Times cewa, Mahatir Muhammad tsohon firayi ministan kasar Malaysia ya yi kira dangane da muhimamncin yin amfani da hanyar koyar da addinin muslunci ta zama ta hadin kai tsakanin al’ummar musulmi ba rarraba kan al’umma ba.
Mahatir Muhammad ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban wani taro da aka shirya a birnin Kualalampour fadar mulkin kasar ta Malysia, domin duba muhimman batutuwa da suke ci wa musulmi tuwoa  kwarya a wannan zamani, da kuma sanin hanyoyin da za a bi domin tunkararsu da kuma warware su ta hanyoyi na hikima.
Ya ci gaba da cewa yanayin da ake cikia  halin yanzu na bukatar fadaka fiye da kowane lokaci, idan aka yi la’akari da iriun makarkashiya da makircin da ake shirya ma musulmi domin ganin bayansu, kuma amfani da hanyoyin wa’azi da ke yada tsatsauran ra’ayi da rarraba kan al’ummar musulmi suna yi wa makiya aiki ne, ko sun sani ko ba su sani ba.
1472548

Abubuwan Da Ya Shafa: Mahatir
captcha