IQNA

Alkawalin Ubangiji Kawar Da Isra’ila A Bayyane Yake A Cikin Kur’ani Mai Tsarki

15:31 - November 18, 2014
Lambar Labari: 1474715
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar malaman gwagwarmaya Sheikh Mahir Hammud ya bayyana Isra’ila da cewa babu makawa za ta gushe bisa alkawalin ubangiji a cikin kur’ani mai tsarki.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-nashrah cewa, Sheikh mahir Hammud babban sakataren kungiyar malaman gwagwarmaya ya jadda cewa  Isra’ila za ta kau babu makawa bisa alkawalin ubangiji a cikin kur’ani wanda kuma ayoyi bayyane suke kan hakan.
Babban limamin masallacin juma’a na garin Saida wanda shi ne babban sakataren wannan kungiya ya tabbatar da cewa abin da haramtaccciyar kasar Isra’ila take aikatawa duk yana daga cikin ayyukansu na zalunci a kan sauran al’ummomi da suka gabata a cikin tarihi, duk kuwa da cewa hakan ba abu ne mai dawwama ba, kuma wannan alkawalin ubangiji ne da baya canjuwa.
Malamin ya ci gaba da cewa zaluncin haramtacciyar kasar Isra’ila a kan al’ummomin palastinu da sauran al’ummomin yanki ya kai matakin da halin yanzu Isra’ila ta fara ganin karshenta, sakamakon jinin bayanin Allah da ta zubar tsawon shekaru, kama daga yakin kan al’ummar Gaza a cikin 2000, 2006, 2008 wanda duniya ta sheda dabbancin yahudawa sahyuniya kan mata da kanan yara, haka nan kuma a yakin baya-bayan da yi da su.
Shehin malamin ya kara da cewa ko shakka babu al’ummar palastinu dsa suke warwatse suna gudun hijira za su koma kasarsu, kuma za su rayu a cikin izza da dauka, kuma karshen zaluncin yahudawa da danniya yana zuwa zuwa.
1474184

Abubuwan Da Ya Shafa: lebanon
captcha